huatong
huatong
umar-m-shareef-nayi-nadama-cover-image

Nayi Nadama

Umar M. Shareefhuatong
patti128huatong
الكلمات
التسجيلات
Nayi nadama, masoyi haa

Ni mata na aure na bida

Na duba banganta ba

Assalam salama farko nayi miki yan mata

Don nayi shiri na da zato za kiyi mini gata

Kauna harda so naki kiban raina ki faranta

Karfin halin ka ashe (iyyeh) ya zarce a misalta

Ka tuno abinda kayi mini a baya naki na manta

Kace da iyaye na zaka zo ka kashe wayar ka

Afuwar ki nake nema

Lalala ba zan yi ma ba

Na canza hali na

A′a bazan aminta da kai ba

Mun dace a soyayyah, ni dake in kin duba

Hadin mu yayo dai-dai in an ganmu ba'a kushe ba

Yarje mana muyo aure zuriyar mu ba zasu ki kyau ba

Hmm umm, ka makara kalaman naka ba zasu shigan ba

Ka dade kana bina da kalmar so naki na karba

Sai a karshe na yarda, ka guje kasa nayi kuka

Afuwar ki nake nema

Lalala ba zan yi ma ba

Na canza hali na

A′a bazan aminta da kai ba

Gaskiya doki na, na hayo gani gaban ki

Yardar ki nake nema, a gida ku na mika sadaki

Ko'a hali zamuyi daidai nasan akwai ki da kirki

Wallahi ka cuce ni, ka tsaya ni nayi maka burki

Yaudara halin ka da kowa ya sani babu mamaki

Yanzu ka juyo kaina kuma na zarce sanin ka

Afuwar ki nake nema

Lalala ba zan yi ma ba

Na canza hali na

A'a bazan aminta da kai ba

Ni na tafi, na tafi, na tafi a baya yanzu na dawo

Da so na hakika na zo gani kiyi mini oyoyo

Kiran ki nake daure ki tsaya fuskarki kidan juyo

Indai wannan ce dubarar taka jeka ka sauyo

Na gane wannan dama ance namiji ba dan goyo

Farin ciki idan nice fari kasa kuka

Afuwar ki nake nema

Lalala ba zan yi ma ba

Na canza hali na

A′a bazan aminta da kai ba

Kiyi mini kallon so na idanu

Ko′a fuska a kayo dubi munyi kamannu

Mai jirar so a fadar ki lallai zaya zaunu

Kokarin ka nake kallo saurayi sannu-sannu

Ganga bakin ki da zaki lallai zaki maganu

Ka iya tsari ammah a kaina ba zakayi tasiri ba

Afuwar ki nake nema

Lalala ba zan yi ma ba

Na canza hali na

A'a bazan aminta da kai ba

Nayi nadama, masoyi haa

Ni mata na aure na bida

Na duba banganta ba

المزيد من Umar M. Shareef

عرض الجميعlogo