menu-iconlogo
huatong
huatong
hamisu-breaker-jarumar-mata-cover-image

Jarumar Mata

Hamisu Breakerhuatong
snodgrassqihuatong
Lyrics
Recordings
Beat amjad records

Ashe da rai nake sonki jaruma Bada zuciya ta ba

Komai ruwa da iska akanki baza daina kewa ba

Idan na samu zarar samun baza na tanka Kowa ba

Ni banga mai harara ba bare na wai ya

Indai akanki ne zana jure wahalar zuwa garin nisa

Da an tabaki a jirani Dan kuwa tilas kazo na dai fansa

Jumurin jiranki nai Dan kizo na kalleki gimbiyar Hausa

Sirri na rayuwata kece kawai da kin kira dana amsa

Zuma a baki dadi gare ta kin bani taki na lasa

Indai a kanki ne nayi nisa dan ba kiran da zan amsa

Tilas ganin mu tilas barin mu kaunar ki tunda nayi nisa

Sam ba batun nasa fasa ko za'a ce mun in bada rai fansa

Tsarin zubinki dai dai ne

Ya kama zuciya ta ne

Ina jin kamar mafarki ne

Ena sonki so mataki ne

Ni banda damuwa idan har zan bude yan idanuna

In kalleki gaki daf dani to me zaya damu kalbi na

Yauwa Za nayi amo tunda na gane kina da tausayina

Dan yanzu na zamo ya Mafatauci mai bidar gurin kwana

Na kwallo shela dan sanar da iya maliya

Kalamaina

Daga zuciya nake kwatanta ina zayya no jawabaina

Idan babu ke ina ne zan saka zuciya ta bar yawan kuna

Kowa da nasa amma kece Ni kece cikar muradai na

Yau gani a ruwa kusa da kada zo ki ceci karko na

Komai da mafuta karda ki saba da furta ban kwana

Inajin ina gani yadda nake sonki yafi karfi na

Nasan a duniya da wanda yake janye duk tunani na

Soyayya rayuwa wani sain sai tazama wutar kuna

Duk wanda ke cikinta shi ne jurau amma fa a wurina

So na faranta rai da ruhi yasa kazama kamar sarki

Kuma rayuwa dawo misali mai kama da a mafarki

Samari muyi hakuri idan har mun samu so musa sauki

Yan mata muyi hakuri idan har mun samu so musa sauki

Masoyi yana da rana ne

Masoyi yana da rana ne

Masoyi yana da rana ne

Midget mix

More From Hamisu Breaker

See alllogo