menu-iconlogo
huatong
huatong
umar-m-shareef-aisha-cover-image

Aisha

Umar M. Shareefhuatong
brennanstownhuatong
Lyrics
Recordings
Aisha

Aisha, a'i

Aisha, a'i

Aisha, Aisha ta

Son ki ya kama zuciya ta, oh

Na yarda tushen farin ciki ce

Ammah in kayi dace

Tunda kiyayya ta zam guba ce

Soyayya waraka ce

Rigafi nayi tuntini

Na samu magani

A masu jinya ku fitar dani

Akwai mai kula dani

Kun ganta nan, tana da alkunya

Abinta nan, ta iya soyayya

Ta kai matuka-gaya, a guri na

Aisha, a'i

Aisha, Aisha ta

Kin fita daban da yanmata

Kece gaban su kinyi rata

In babu ke a kai ni makabarta

Ba zan iya aure da kowa ba

Kullum tarairaiya

In anka bani ke

Banso ki sha wuya

Zanyo kula dake

Abinda kika so zanyi miki shi

Wanda baki so zana barshi

Bazan saki kuka ba

Aisha bazan baki haushi

Zaki ga gata Aisha ta

Aisha sarauniyar mata

Akwai ta da kyan kallo

Tauraruwa in ta bullo

Diyar Fulani yar fillo

Ku ganta kyakwawa

Son kowa

Mai ladabi ga kowa

Bata da damuwa

Bata raina kowa

Yanmata ku kauce

Wannan ta daban ce

Kwalliyar ta daban ce

Tafiyar ta daban ce

Karta sani na zauce

Aishar, Aisha ce

Nina fada kin fisu

Kece gatan su

Aisha dawisu

Na baki suna sarauniyar mata

Aisha

More From Umar M. Shareef

See alllogo