Alkalami dashi nake rubutun
Sunanki, in bai wasu suyi karatu
Alkalami dashi nake rubutun
Sunanka, in bai wasu suyi karatu
Farko na, da karshe na soyayya ce
Nasan kin fini sani
Tarko na, danayi dani ke ya kama domin ke zamo magani
Babu sani babu sabo gun wanda ke shirin bata ranki zai gani
Hula ta, da yar sanda ta
Bani in rike a hanu ke ko ki biyoni baya
Soyayya ta fito
Daga zuciya yanayin danake ambato
Zanyi murna in dai kace nice gwanarka
Farin ciki sai ya fito
Babu ni ba nuna jira
In dai har kabani so sai na shahara
Zana amsa kiranka
Damuna harda kaka
Munyi karo
Tafiyarmu iri daya
Shi mai far maki, a cikin dare
Baya so ko kadan yaji kukan kare
Ingo zarena, karda ki warware
Dadin abinci, asa shi cikin tire
Miko hanu nade duka mu tsinko fure
Asalina chan dole zana ankare
Waiwaya baya
Lulubi mai kyau sai dai abarwa masoyiya
Alkalami dashi nake rubutun
Sunanki, in bai wasu suyi karatu
Gani da dan salona
Zanyi wa masoyina, aljana gurina
Kai zana rike abina
Kowa nasa yake so ni kai na nuna
Allah raba mu da bata suna
A gurin mutanen da basu da wata rana
Sanadin kauna, yasa na gane toshe na
A duniya
Alkalami dashi nake rubutun
Sunanki, in bai wasu suyi karatu
Alkalami dashi nake rubutun
Sunanka, in bai wasu suyi karatu
In bai wasu suyi karatu