Ki saurareni, sako daga zuciya
Ki tarbeni, kiji ko me zan fada
Sako, sako daga zuciya
Sako, sako daga zuciya
Burina shine na mallakekini
Saurara kiji, sakonga nakine
Bawani jin dadi, mai kyau in baki ne
Bawata soyayya mai kyau, in baki ne
Babana da mamana sunyi na'am da ke
Sunce aurenmu za'ayi taho dani da ke
Mun shaku da juna, alkawarinmu mun rike
Sako daga zuciyata tace na bayyana
Lalala
Nayi gami dake ne, a sanda banyi zato ba
Sai gashi zuciyata ta kama banyi amo ba
Kin kafa mini tarihi wanda ba'a taba min ba
Ko ina zani nake kar kizo garen ki duba
Nasan Allah ya sa min sanki, bazan cire ba
Soyayya ta tambayeni ban jima ba
Sabon shiga zakice min, koko ban iya ba
Kin san banida magani sai ke, yaki zo taho mu zauna
Baby, ahhh
Allah sarki so, mai saka zuciya ciwo
In ya shige ka, kayi kama da mai kiwo
Kullum nazari na, a yaushe zamuje yawo
Da ni da abin sona, wadda nake yiwa awo
Kinada kalaman so mai saka zuciya iyo
Ni nafada kogin sonki, ciki na zagaya
Daga zuciya naji kiranki, kince na waiwayo
Sakonki ya isheni, ya zaga ko ina
Baby, ahh
Gimbiyata kece, a gidan gaban motata
'Yar uwa ina sonki, shiyasa muka samu fahimta
Batutuwana kece, batsokanai wauta
Abokanai na sunce, wai zuciya kinka asirta
A dan zaman, da mukayo dake nagane
Kinada kyan hali, hakan yasa na manne
Kice kinka ce mani ko babu kayan daki
Zamuyi zaman mu lafiya lau da juna
Oooh
Sako, sako daga zuciya
Sako, sako daga zuciya