Ni'imar Allah
Yau gamu nidake muna a ciki
Wa zamu godewa?
In bashi ba babban sarki
Shi ya hadamu
Yau gashi ni dake muna farin ciki
Gashi har nabaki gun zama
Cikin zuciya kike mulki
Giyar santa nasha, samari wazaya mun birki?
Zuciya ta kamu, hanta ta kamu, baki ya kamu da sunanki
Mallakina raina
Komai nawa kaine ka rike
Bakina, kullum ambaton sunanka yake
Ba wace zata rabeka
Idan tai hakan akwai sake
Ni kadaice taka
Matso-matso kazo in ma take
Autan maza, nauyina duka zakana dauke
Zan zama dakai, nai rayuwa dakai
Domin nai sabo da soyayya-aa-ah
Buri na zuciya, rabo dani dake baza nayi ba
Bazana sauya ba
Bazana sauya ra'ayina ba
Dan ko kin zam min, farin gani garan abun duba
In baki wa zana kalla
A zuciyata ke naba lamba
Idan mukayi aure, mata bazana kara kallo ba
Kin zamo jigo na
Uwar yarana, miko na damke, amanarki
Duk soyayya, gareka kai dai ne na bada
Aurena idan kayo ba batun ganda
Dan zana bada soyayya
Gareka duka kunya zan kauda
Dan ko ni na dauke ka, cikin maza kazam gwanda
Nai godiya, ga wanda ya hadamu tun chan da
Yau dani dakai
Mun hada kai
Mun zam lambar dai, a duniya