Kece nakewa kallon soyayya
Kaine nakewa kallon soyayya
Dukkan dadi bai wuce ace, kaso a so ka
Yar lelena makida madadi, ke zanwa barka
Burin kowa yayi dace da irin mutum mai irin harka
Ni ga tawa, ban boye ba
Komai na bida gunta bana rasa ba
Batada aiki sai kyautata min
Ohh ahh
Kyakkyawar zuciya take hanu
Ni dakai zani hau gado
Jarumina bai tsoron jido
Duk a cikin so nemo ungo koredo
Hasken rayuwa salatin annabi ne
Dacen lahira soyayyar nabiyyu ne
Ohh, ahh
Na rike tutar so ta jani
Zo da majanyi ki jawoni
Babu fushi in kika kamani
Babu damuwa in kika goyani
So baya hana kyau koko muni
Nayi zufa baby ke ke share min (ahh)
Ai keke dadada min (ahh ooh)
In na fito ka fito wa zai tare, babu shi
Mai neman fada, akwai shi da tsoron nushi
Muyi addu'a Allah ya tsaremu da kyashi
Mahadin rayuwata kaine
Dan saurayina kyakkyawa ne
Baya kule-kulen wuta ne