menu-iconlogo
huatong
huatong
abdul-d-one-rikicin-aure-cover-image

Rikicin Aure

Abdul D Onehuatong
robstirling70huatong
Lirik
Rakaman
Rayuwa zatayi kyau ni dake, rikicin aure bama ciki

Mu kasance tare a ko yaushe, ni dake ba mai yin gardama

Rayuwa zatayi kyau ni dakai, rikicin aure bama ciki

Mu kasance tare a ko yaushe, ni dakai ba mai yin gardama

Soyayya ba'a karatu, in ka iya tana kanka

Komai zakayi, yi shawara yafi kayi gaban kanka

Gunki na doso da tambura, nafiso ki tattaka

Ban so kibani tazara, in kika yi zan hauka

Wasa kala kala, zamuyo dake duka

Nasaba bada zuciya, a yanzu kema ga taki

Oohh

Sarkin yaki, a sannu-sannu so ya girma

Nice mai girki, kai kuma ka wuce gun nema

Abincin girma, kaci tuwo miyar ga nama

Naji dadi-dadi, kace nice ta hannun dama

Nisan kwana Allahu yayi ma

Dadin kallo kazarce korama, hakane

Kin iya satar zuciya (oho-oho-oho)

Zani kiraki guda holiya (oho-oho-oho)

'Yanmata kin masu bulaliya

Kece dai burin duniya

Nai babban kamu nan masoyiya

Zani baki kaina, in saki a jiki

Shi mummuna bashi kwalliya (koyayi sai an gane)

Kyawun kallo na gamai ado, komai kai dai-dai ne

Mace batayi in ba salo, koko nai karyane

Saurayi kai ne na tsayar gwani, kowa ya kasa kunne

Mata in bamu ba gida (haka ne)

Matsayinka daban ne (daban ne)

Oooh

Rayuwa zatayi kyau ni dake, rikicin aure bama ciki

Mu kasance tare a ko yaushe, ni dakai ba mai yin gardama

Lebih Daripada Abdul D One

Lihat semualogo