menu-iconlogo
huatong
huatong
เนื้อเพลง
บันทึก
Mm, mm, mm, mm

Mm, mm, mm, mm

Lalala-lalala

Lala

Auta kece ra'ayina, a mukamin farko (ooh ahh)

Auta kaine ra'ayina a mukamin farko (ooh ahh)

In na tuna labari domin ke, in baki kisha ko zai dadi

A sannu a sannu muna tafiya, inayi maki taki mai dadi

Bakimin ba'a auta, kin wuce su auta

Ga kyau ga da'a auta, lallai kin taka sa'a auta

Cikin bacci, nayi mafarki nasanki

Ashe kema kina so na, mafarki ya zamo gaske auta

Auta kaine ra'ayina, a mukamin farko

Bari kaji sabon suna a soyayya, dazani sama

Natsu kaji sabon taken soyayya, dazan buga ma

A zuciya kayi kamar wani ingarma, mai sa maza su suma

A gareka nayo karatun samu, kaine kace na nema

Dan autana, mai kauda takaici na

A kowace rana, ban canza maka suna auta

Dan adam ajizi, kowace rai na bidar kara

Mai wa'azi nasiha yake, ko a ina kaji saurara

Shi dan adam iri-iri, wani halinsa akwai gyara

Wani gyaran ma baya so, kullum zunubi ya tattara

Ya Allah ka shiryemu, da lahira musha gara

Allah yasa na aureki, mai tarbiya cikin mata

Wayyo kaina, kasa naji wani tsoro

Kai magana cikin hankali, har kunne ya sauraro

Mai nazari yake gane, nisan tafiyar dan kwaro

Almajiri ya dau allo, dan boko kuwa sai biro

Soyayyace silar aure, a cikin haka har azo taro

Haduwarmu dakai akwai murna, dan nasan nazamo mata

เพิ่มเติมจาก Abdul D One

ดูทั้งหมดlogo