menu-iconlogo
huatong
huatong
umar-m-shareef-share-hauwaye-cover-image

Share Hauwaye

Umar M. Shareefhuatong
steveg5489huatong
เนื้อเพลง
บันทึก
Share hawayenki, amarya share hawayenki

Miya ya dameki?

Amarya wai miya ya dameki?

Yau ake daura aurenki

Ranar farinciki gareki

Yau dake da ′yan uwanki

Ango ya biya sadaki

Saura a kaiki daki

Je ki gaida iyayenki wanda su suka haifeki

Masu tarbiya gareki

A yanzu ke dubanki

Farinciki sun baki

Basu so suga kukanki

Gashi yau ranar bikinki sun ga muna susuronaki

Ki biyayya gurin ango

Tunda yanzu shine jigo

A gareki ya zam ango ma'ana mai kwarar daki

Kinyi aure ibada

Kunne ido ki kauda

Kinji-kinji duk ki zubda zancen masu son su kulla yaki

Ango amarya nai maka barka

Kyakykyayawa ce amarya hakika

A gida na tarbiya aka dauka

Kwalliya gurinta sai son barka

Lokaci yasa rawar dana taka

Auren Allah yasa albarka

Farinciki kuke ciki

Maza da mata sun zo

Mai bakinciki-bakinciki

Muko bishi da kanzo

Ranar biki yau ake biki

Maza da mata sun zo

Mata kuban guda

Muyi rawa muyi rawa muyi rawa

Har wani kamshi ma tashi yake

Naga kawaye har juyi suke

Abokai su ma sai taku suke

Iyaye sai sa albarka suke

M. Shareef mai waka

Yanzu ma muka fara

Kowa yazo ya taka

Dan haka nan muka tsara

Nai haka nai haka

Kuma kuyi haka kuyi haka

Mata kuzo da girgiza

Mazaje sai ku a gaza

Amarya zo ki rangaza

Ango kizo Ki ingiza

เพิ่มเติมจาก Umar M. Shareef

ดูทั้งหมดlogo