menu-iconlogo
huatong
huatong
bash-neh-pha-duniya-cover-image

Duniya

BASH NEH PHAhuatong
sherrellssmhuatong
Lời Bài Hát
Bản Ghi
Duniya

Bash Neh Pha

Duniya

Duniya

Life

Hour-hour wasu plasma wasu yakubu tv

Mutane daban daban

Wani babu gemu babu tinbi

Tsoho zai fada ma duniya a da sune sababi

Halitu ma sun banbanta

Gefen giwa gefen zabi

Bai faru ba

A ce wa kowa layi daya zai bi

Indai kai kaje a jirgi wani trailer ne zai bi

Wani ci da gwamnati

Wani da saida kayan baby

Wani ya bi hanyar office

Wani hanyan gona zai bi

Wani in ya ci ya koshi takan naman kaza zai bi

Wani zai ci zogale wanda kudadai suke bi

Wani san duniya ne ma yasa kun daina sa hijabi ne

Neman kudi hadda yankan kai kun manta ma hisabi

Hanyar hawaiwa na fito hanyar mutuwa ne zan bi

Duniya karama che kamar ramin da tsinke zai bi

Kana jira sai ka tsufa zaka ce wai Allah zan bi

In ka bi baba da Mama kaine Albarka zai bi

Kana kwana a katifa wani tabarma shi zai bi

Kana neman na sutura wani na abinci zai bi

Layin da Allah ya zana dolle shi ne bawa zai ba

Kar ki hallaka ni (duniya)

Kina rikita ni (duniya)

Kina da dadi (duniya)

Kai baki da dadi (duniya)

Kar ki hallaka ni (duniya)

Kina rikita ni (duniya)

Kina da dadi (duniya)

Kai baki da dadi (duniya)

Dolle jinjiri zai tsufa zai kodai ya yamushe kaga kamar an matsa paper

Ya yan samari na tsiya dan jinin su yana kumfa

Minene bahaushe ya fada?

Komai nissan jifa

Wasu don talauci duniya suna cikin masifa

Wani ba Ido ba kafa amman ka duba kai fa

Wani ba hannu ba kunne bale ya tuka tifa

Duniya wani na kauye inda babu wutan nepa

Nazi zuma

Ban dutsen maganganu in jefa

Wasu sun dauki gulma a nan da chan suje su jefa

Gwanda kai ka ci tuwo

Wanda ya rasa fatai fa

Kar ran ka ya bacci kana keke in kaga bespa

Duniya ce zaka je ka sai motor kuma ka pimper kayi gida ka sa iyalin ka

Ka kulle kofa wani bai da shi gidan haya a nan yake ta tsufa

Kuna san labarin duniya ku ban biro da paper

Wani ba gida sai karin aure da tsabar masifa

Wai Sallah ana jiran mai kudi

Lahira akwai fa tsakanin mu da banbanci

Rediyo da woofer dan mama bakin magana

Yau dolle zaku sha fama

Kar ki hallaka ni (duniya)

Kina rikita ni (duniya)

Kina da dadi (duniya)

Kai baki da dadi (duniya)

Kar ki hallaka ni (duniya)

Kina rikita ni (duniya)

Kina da dadi

Kai baki da dadi

Bash Neh

Gwanda kai samu haihuwa

Mai zagin kashin yaro, yi tunannin

Wanda bai da shi ga shekaru sun karu

Yanzu kai kafara girman kai dan kazama tauraro

A che dai yanzu a ko ina

Kune fasa taro

Ka wuce shan ruwan rijiya

Sai dai ruwan faro

Ka bar yan uwa da abokai

A chan da durin baro

Kar ka manta yan uwan ka ma

Akwai ma tallan goro

Dan mama ku bani lokaci

Yanzu zan je in karo

Kar ki hallaka ni

Kina rikita ni

Kina da dadi

Kai baki da dadi

Kar ki hallaka ni

Kina rikita ni

Kina da dadi

Kai baki da dadi

Music at 360hausa dot com dot ng

Nhiều Hơn Từ BASH NEH PHA

Xem tất cảlogo