menu-iconlogo
huatong
huatong
umar-m-shareef-rayuwata-cover-image

Rayuwata

Umar M. Shareefhuatong
oproedekehuatong
Liedtext
Aufnahmen
Lallalla

Lalalalalala

Lalalalalala

Lalalalalala

Rayuwata kece

Rayuwata kaine dai-dai ni, ba cuta ba cutuwa

Rayuwata kaine

Rayuwata kece dai-dai ni, ba cuta ba cutuwa

Ke na saka bangon littafi na

Wanda yake dauke da duk labarina

Auren ki karshen lissafi na

In na rasa ki rannan an rufe babi na

Kun ji sai kuyi shaida

Rayuwa na bada

Na aminta ku yada

Mai ki idon sa ya kauda

Ban dauka ba, kar in shiga damuwa

In ba kai ba, na fada ruwa

Son ka a raina tamkar zanen zabuwa

Ba batun ka dishe ko kayo goguwa

Ana ta kawo suka mai ke faruwa?

Mai makon ka rage kullum sai karuwa

Na samo yarinya kyakkyawa

Kun gan ta son kowa

Ta sa mini jindadi

In ta fito, kowa na rububi gun kallon ta

Yayi ta rawa, jikin su suna kaudi

Oyoyoyo

Na samo dan yaro kyakkyawa

Kun gan sa son kowa

Ya sa mini jindadi

In ya fito, kowa na rububi gun kallon sa

Yayi ta rawa, jikin su suna kaudi

Da Turanci in zan kira ki "darling" tsari na

Da Larabci "qurrata aynun", sanyi na ido na

Faransanci "mon amour", shine zabi na

Kin zarce yadda suke tunani a cikin raina

Da Turanci in zan kira ka "baby na"

Da larabci sannu "nurul qalbi na"

Faransanci "ma chérie" abin kauna

Ka zarce yadda ake tunani a cikin raina

Rayuwata kece

Rayuwata kaine dai-dai ni, ba cuta ba cutuwa

Rayuwata kaine

Rayuwata kece dai-dai ni, ba cuta ba cutuwa

Idanu na basu gani in baka nan

Idanu na basu gani in bakya nan

Mehr von Umar M. Shareef

Alle sehenlogo