(M. Shareefi)
Dangin amarya ku taso
A yanzu ku ne da fili
Dangin amarya ku taso (fili-fili-fili-fili)
A yanzu ku ne da fili
Wannan dangin amarya ne
Sune kan gaba
Jini gami ne da hanta
Wa zai rar raba?
Daka yana nan ga mata
Ba Danjuma ba
Kitso mai gashi ake wa
Ba kwikwido ba
Ruwa shi ke tura bango (amarya)
Biki ba a kai wa raggo (amarya)
Lokaci mu dubo agogo (amarya)
Naku ne ku dangin amarya
Dangin amarya ku taso
A yanzu ku ne da fili
Dangi ina ji daku ni
Ban yashe ku ba
Daku nake fahari na
Nake cigaba
Idan mutum bai da dangi
Bazai kaini ba
Duk mai riko da zumunci
Ba zai fadi ba
Amarsu dangin ki sunyi (amarya)
Bikin ki Allahu yayi (amarya)
Kuyo rawa kuyi ta juyi dangin amarya (amarya)
Tunda yanzu kune da fili (amarya)
Dangin amarya ku taso (fili-fili-fili-fili)
A yanzu ku ne da fili (fili-fili-fili-fili)
Dadin zuwan arziki
Iske wa mai mallaki
Ta faru yau ne biki
Ikon sa dai khaliki
Koh zasu koh su 'ki
Gidan su anyo biki
Mu bar batun laulayi (amarya)
Kina cikin yanayi (amarya)
Amarya me za kiyi? (Amarya)
Murna kawai zakiyi (amarya)
Dangin amarya ku taso (fili-fili-fili-fili)
A yanzu ku ne da fili
Mata iyayen biki
A gaida kirjin biki
Gida, gidan arziki dangin amarya
Wannan bikin naku ne
Farin cikin yar ku ne
Murna a yau dole ne
Mu taya amarya
Dangin amarya ku zo (amarya)
Ku taru ku dandazo (amarya)
Da rausaya zaku zo (amarya)
Farin ciki sai yazo fuskar amarya (amarya)
Dangin amarya ku taso (fili-fili-fili-fili)
A yanzu ku ne da fili
Dangin amarya ne
Su masu hali ne
Kuma masu girma ne
Basu gaji karya ba
Ga shigar su tsaf-tsaf-tsaf
Takun su taf-taf-taf
Suffar su mai kyawu
Ya baza a kalla ba?
Sun wanku sun wanka
Dangi cikin rinka
Jama'ar amarya ne
Ba a sa da kowa ba
Ga Dollar da Nairori
Tafiyar su ba sauri
In ana batun Naira
Ba a barku baya ba
A wuyan su sarkoki
Kwalliyar gidan sarki
Komai nasu kan saiti
Ni banyi kage ba
Iyayen amarya
Yayyen amarya
Kannen amarya
Kawayen amarya
(Oh my God, Sultan on the beat)